Najeriya ce ta uku da aka fi fama da ta'addanci a duniya





Wani rahoton hukumomin kasa da kasa kan ayyukkan ta'addanci ya ce Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen da suka fi fama da ta'addanci a duniya.
Rahoton wanda cibiyar bunkasa tattalin arziki da zaman lafiya ta IEP da ke birnin Sydney ta fitar ya nuna cewa bayan kasashen Iraqi da Afghanistan, Najeriya ce a kan gaban wajen yawan mutanen da suka mutuwa saboda hare-haren da ke da alaka da ta'addanci.
Sai dai rahoton ya ce an samu raguwar yawan adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren ta'addanci idan aka kawatanta da shekarar 2018.
Amma kuma rahoton ya ce ta'addanci na ci gaba da yaduwa a kasashe.
A cewar rahoton, a Najeriya an kai hare-haren ta'addanci 562 da suka kashe mutum 2,040, adadin da ya kai kasar matsayi na uku a jerin kasashen da ke fama da hare-haren ta'addanci.
Afghanistan ce ta daya a duniya da aka fi fama da hare-haren ta'addanci inda aka kai hare-hare 1,443 da suka kashe mutum 7,379, sai Iraqi da aka halaka mutum 1,054 a hare-hare 1,131.
Hakan nafin an fi kai hare hare a Najeriya fiye da Syria da ke matsayi na hudu inda aka kashe mutum 662 a hare-hare 131 na ta'addanci.
A nahirar Turai, inda rahoton ya ce ba a fuskanci hare-haren ta'addanci ba a 2018, adadin wadanda suka mutu ya ragu daga 200 zuwa 62.

(c) BBC Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Insecurity in Zamfara: The Silent Crises in Dansadau Emirate

ADC Begins Distribution of Membership Cards, Registers Across 14 LGAs

An Urgent Call to Authorities on Graduation Celebrations